Sai miya ta kare

Assalamu alaikum abokan aiki!

Gaisuwa ta musamman ga @danzubair da @ranbash1 !

Na san dai kuma masu kishin harshen Hausa ne kamar ni. Saboda haka, ya kamata mu mike tsaye tun da gashi mun samu wannan dama ta fassara manhajar hada shafukan intanet mafi farin jini a duniya – watau WordPress.

Godiya ta musamman ga Allah SWT da ya bamu wannan dama, kuma na yi imanin cewa zamu sauke wannan gagarumin nauyi da muka dauka.

Ba zan manta da Petya Raykovska (@petya) ba, da sauran mambobin Polyglots Team domin taimakon da suke bamu.

Na bude mana shafin sadarwa a Slack.com, domin muma mu iya samun taimakon da muke nema a wajen sauran kungiyoyin dake fassara WordPress. Sunan shafin “WordPress Hausa” kuma yana nan: WPHausa. zaku ga sako a imel dinku nan ba da jimawa ba.

Da karshe, ina fatan zamu yi amfani da wannan damar domin mu karu da juna ta hanyar mutunci, ba tare da wasu matsaloli ba. A koda yaushe, a shirye nake da in bada hadin kai na wajen tallafa ma wannan aiki.

Na gode!

#fassara, #hausa, #tarjama, #translate, #wordpress